Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci a kasar Faransa yay i kira ga dukkanin musulmi da su hada kais u watsar da duk wani banbanci da ke tsakaninsu domin kuwa abin da ya hada su bai raba sub a wato sheda babu sarki sai Allah da annabcin manzo da kuma littafi guda kur’ani.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na press TV cewa, Sheikh Sango babban malamin addinin muslunci a kasar Faransa yay i kira ga dukkanin musulmi da su hada kais u watsar da duk wani banbanci da ke tsakaninsu domin kuwa abin da ya hada su bai raba sub a wato sheda babu sarki sai Allah da annabcin manzo da kuma littafi guda kur’ani, kamar yadda alkila guda suke kallo su yi salla, wata guda ne suke yin azumi.
A bangare guda kuma kungiyar kasashen Musulmi ta OIC za ta tura tawaga ta musamman zuwa kasar Bama ko kuma Myanmar domin jin dalilan gwamnatin kasar na bayar da umurnin korar musulmi daga kasar. A lokacin da yake gabatar da jawabi ga mahalarta wani taro da kungiyar ta shirya a yau lahadi a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, Babban Magakatarda na Kungiyar Ekmaluddin Ihsa-noglu ya ce babbar manufar wannan tawagar da za a tura zuwa kasar ita ce tattaunawa da Hukumomin kasar kan yadda za a warware wannan matsala ta ruwan sanyi.
Su dai hukumomin kasar Myanmar sun bayyana cewa musulmin kasar 'yan kabilar Rohingya ba cikakken 'yan asalin kasar ba ne, saboda haka suka umurce su da su bar kasar, lamarin da kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 80, yayin da kungiyoyin kasa da kasa da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka rufe ido kan wannan abun assha da ke faruwa a kan musulmi.
1071407