Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Elnashra, cewa babban sakataren kungyar gwagwarmaya ta hizbulalh Sayyid Hasan Nasrullah zai gabatar da wani jawabi dare yau inda zai tabo muhimamn batutuwa da suka danganci halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya da kuma hankoron da kasashen yammacin turai suke yin a ganin cewa sun rikita yankin baki daya kamar dai yadda suka tsara tare da abokansu na yankin gami dsa karnukan farautarsu.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci i ya bayyana cewar irin ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu ya biyo bayan riko koyarwar Alkur'ani da kuma shiriya ta Ubangiji ne. Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan yadda wasu suka riki al'adu na abin duniya wadanda suka ginu bisa tushen abin duniya da kuma nesantar kyawawan halaye, Jagoran cewa ya yi: Daya daga cikin misalan da ke tabbatar da rashin gaskiyar ikirarin da kasashen yammaci suke yi na riko da kyawawan halaye da kuma kare hakkokin bil'adama shi ne shirun da suka yi dangane da kisan gillan da ake yi wa dubban musulmin kasar Myammar. Jagoran ya yi kakkausar suka da irin yadda kasashen yammaci suka yi shiru da ci gaba da nuna halin ko in kula dangane da irin kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar musulmi na kasar Myammar din inda ya kirayi al'ummar musulmi da su taimaka musu ta dukkanin hanyoyin da suka saukaka.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Tsawon karnonin da suka gabata, a duk inda al'adun kasashen yammaci suka sanya kafafunsu, babu wani abin da za a gani in banda fasadi da amfani da bil'adama a matsayin kayan aikin cimma manufofi na duniya. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Za a iya samun daukaka, jin dadi, ci gaba na duniya da lahira, kyawawan halaye da kuma samun nasara a kan makiya ne kawai ta hanyar riko da kuma aiki da koyarwar Alkur'ani mai girma.
Har ila yau kuma yayin da yake magana kan irin farkawar da al'ummar musulmi suka yi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Matukar dai al'ummar musulmi suka sami damar tabbatar da ci gaban da ya ginu bisa asasin koyarwa ta Ubangiji da kuma da kyawawan halaye, to kuwa bil'adama za su sami sa'ada da kwanciyar hankali. ya bayyana farin cikinsa da yadda ake ci gaba da samun karuwar kaunar Alkur'ani a cikin zukatan al'ummar Iran musamman ma matasa don haka sai ya jaddada wajibcin tunani sosai cikin ma'anoni na Alkur'ani da kuma aiki da su.
1072010