IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Harin Ta'addanci Kan Gidan Talabijin A Syria

9:43 - August 08, 2012
Lambar Labari: 2388099
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullaha kasar Lebanon ta yi Allawadai da harin ta'addancin da aka kai kan ginin hukumar radio da talabijin din kasar Syria a birnin Damascus fadar mulkin kasar a jiya da rana tsaka a yunkurin da kasashen yammacin turai suke yi na tarwatsa kasar.

Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tasar talabijin din Almanar, cewa kungiyar gwagwarmaya ta hizbullaha kasar Lebanon ta yi Allawadai da harin ta'addancin da aka kai kan ginin hukumar radio da talabijin din kasar Syria a birnin Damascus fadar mulkin kasar a jiya da rana tsaka a yunkurin da kasashen yammacin turai suke yi na tarwatsa kasar tare da karnukan farautarsu da ke yankin.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi zai isa kasar Turkiya domin tattaunawa da mahukumtan kasar a yau . Rahotanni sun bayyana cewa ministan na kasar Iran Salihi zai je kasar Turkiya ne domin tattaunawa game da batun iraniyawa guda 48 masu ziyara da masu dauke da makamai suka kamasu a kasar Siriya, kana zai jadaddawa mahukumtan kasar nauyin da ya rataya a wuyansu, ganin su na daga cikin masu goyon bayan yan tawayen da ake kira jaishul hur a kasar Siriya da suka kame iraniyawan.

A bangere guda kuma tuni babban sakataren tsaron kasar iran Sa'id jalili ya isa kasar Siriya domin tattaunawa da shugaban kasar Bashar Asad kan muhimman batutuwa da suka shafi kasashen biyu, da kuma batun iraniyawa masu ziyara guda 48 da yan tawayen suka kama a kasar.

Yanzu haka dai yan ta'adda suna ci gaba da rike da Iraniyawa da suka kame tun ranar Asabar da ta gabata bias hujjar cewa suna zarginsu da taimaka ma gwamnatin shugaba Bashar Asad, wanda ya zama bababn karfen kafa ga manufofin siyasar kasashen yammacin turai a yankin gabas ta tsakiya.

1073111




















captcha