Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habrta cewa, ya nakalto daga shain sadarwa na yanar gizo cewa, Hamid Muhammadi mataimakin ministan ma’aikatar kula da harkokin al’adun muslunci a jamhuriyar muslunci ya bayyana cewa shirya gasar karatun kur’ani da ta ke banci matasa daliban jami’a na kasashen musulmi na da matukar muhimmanci kamar yadda hakan yana kara karfafa gwiwar daliban wajen mayar da hankali ga harkokin kur’ani mai tsarki.
A taron manema labarai da ya gabatar a yau lahadi, kakakin kwamitin shirya Taron Koli na Kungiyar Kasashen Duinya 'Yan Ba Ruwanmu da za a gudanar daga ranar zuwa ga wannan wata na Agusta a nan Tehran, ya ce Jagoran Juyin juya halin musulunci na Iran ne wato Ayatullahil Uzma Sayyed Ali Khemenei da kuma Babban Magakatarda na Majalisar Dinkin Duniya na daga cikin wadanda za su gabatar da jawabai ga mahalarta wannan taro.
Kakakin kwamitin shirya wannan taro Mohammad Reza Forqani ya ce kawo yanzu akwai shuwagabannin kasashe 31 da suka tabbatar da aniyarsu ta halartar wannan taro, wasu kasashe za su turo ministocinsu ne na harkokin waje, sai kuma wasu kasashe 4 da za su turo tawagogi na musamman, sai wasu kasashen da jakadojinsu da ke nan Iran ne za su wakilce su a wannan taro wanda shi ne irinsa na karo na da za a gudanar. Ita dai wannan kungiya ta 'yan ba ruwanmu an kafata ne a shekara ta a kasar Yougoslavia, kuma a halin yanzu tana da kasashe mambobi da kuma wasu kasashe da ke a matsayin 'yan kallo, kuma babbar manufarta ita ce samar da ci gaba, tsaro da kuma tattalin arziki a tsakanin kasashe mambobinta. A game da taron na Tehran kuwa, shugaban kasar Rasha Vladamir Putin da kuma takwaransa na Turkiyya Abdullah Gul ne aka gayyata a matsayin manyan baki.
1074046