IQNA

Gum Da Baki Da Kasashen Duniya Suka Yi Kan Kisan Musulmi A Myanmar Abin Kunya Ne

17:59 - August 09, 2012
Lambar Labari: 2389116
Bangaren kasa da kasa, bababn abin kunya ne yadda kasashen duniya suka yi gum da bakunansu kan cin zarafin da ake yi wa mabiya addinin muslunci a kasar Myanmar duk kuwa da raya kare hakkin dan adam da ake yi a duniya kasantuwar cewa su masu amfani ba ne ga siyasar kasashen.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta, ya zanta da daya daga cikin yan majalisar dokokin kasar Iran, Ali Iranyuvar wanda ya bayya cewa bababn abin kunya ne yadda kasashen duniya suka yi gum da bakunansu kan cin zarafin da ake yi wa mabiya addinin muslunci a kasar Myanmar duk kuwa da raya kare hakkin dan adam da ake yi a duniya kasantuwar cewa su masu amfani ba ne ga siyasar kasashen musamman ma na turai daga cikinsu.
A tsammani shi ne addinin Budda wanda ya yi imani da halin kirki da kyautatawa halittu, da s u ke kira Neravana, su zama masu kyautatawa abokan zama da su. A lokacin da 'yan taliban su ka tarwatsa gumakan Budda a Afgahnistan wadannan musulmin da ake kashe wa a yanzu sun yi Allah wadai da Taliban su ka kuma bayyana abinda su ka yi da cewa keta ce da mugunta. Daruruwan shekaru musulmin kasar Thalidan su ka yi suna rayuwa da mabiya addinin Budda, amma ana samun sauyin siyaya a cikin kasar sai abokan zamansu su ka ci amanarsu da fara kashe su. Da gangan ake son nuna cewa a duk inda musulmi su ke a duniya masu son tada hankali ne. Wannan siyasa ce yammacin turai ke amfani da ita a lokaci mai tsawo. Wannan kuwa ba shi ne karon farko ba da aka yi wa musulmin mayammar kisan kiyashi.
A tsawon lokacin mulkin sojan wannan kasa sun zama zakaran gwajin dafi na nuna kiyayya a gare su. Abin da ake sa ran kungiyoyin kasa da kasa su aikata shi ne kawo karshen wannan irin kisan da ake yi wa musulmin muyammar, saboda su ma su rayu daidai da kowace al'umma a duniya. Idan a tsawon shekarun baya har zuwa 2010 gwamnarin Mayammar ta kasance a cikin killcewa daga kasashen duniya saboda mulkin soja na kama-karya, to shakka babu kisan kiyashin da ta ke yi wa musulmi zai maida ita zama mai laifi akalla a idon sauran musulmin duniya. Musamman ma dai kasashen musulmin kuda maso gabacin Asiya kamar su Indonesiya da Malasia da su ke a wannan yankin ba za su ci gaba da zama 'yan kallo ba.
1074053
captcha