IQNA

Kungiyar ISESCO Ta Yi Suka Kan Yunkurin Yahudawa Na Canja Wa Bagiren Msallacin Qods

14:41 - August 11, 2012
Lambar Labari: 2390232
Bangaren kasa da kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta kasashen musulmi ta yi kakakusar da yin Allawadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce tana shirin dauka na canjawa masallacin Qods wuri domin ta huta daga abin da ta kira fitinar palastinawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, babbar kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta kasashen musulmi ta yi kakakusar da yin Allawadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce tana shirin dauka na canjawa masallacin Qods wuri domin ta huta daga abin da ta kira fitinar palastinawa da suke mallakar wurin da ma sauran msuulmi.
A wani bayanin na daban kuma duk da cewa shugaban Amurkan yana nuna irin kokarin da yake yi wajen ganin HKI ba ta yi gaba gadi wajen kawo wa Iran harin soji ba, to amma kuma duk da hakan yana ci gaba da cewa ba su kawar da wannan batu na kawo hari din ba hakan da nufin kara matsin lamba a kan Iran. To amma a fili yake sannan kuma su kansu Amurkawan sun san cewa Iran ba ta nufin mallakan makaman nukiliya. Babbar manufar dukkanin wadannan abubuwa dai ita ce dakatar da Iran daga irin ci gaba mai ban mamaki da take samu a fagen ilimi da fasaha don haka Amurka da kawayen nata musamman suka dauki wannan siyasa ta kashe masanan nukiliya da kuma barazanar kawo harin soji ko za su cimma wannan manufar.
Ko shakka babu kamar yadda ministan harkokin wajen HKI ya bayyana ne a ziyarar da ya kai Amurka a watan Fabrairun da ya wuce don neman goyon bayan Amurka kan amfani da karfi a kan Iran inda ya ce tana da zabi daban-daban wajen fada da shirin nukiliyan na Iran. Duk da cewa batun kawo hari kan Iran ba abu ne mai sauki ba a gare su sakamakon abin da zai biyo bayan hakan, to amma ko shakka babu amfani da hanyar barazana da kisan gillan suna daga cikin hanyoyin da suka dauka don cimma bakar aniyarsu kan Iran.
Akwai shaidu da yawan gaske da suke nuni da yadda kungiyar leken asirin ta yi amfani da wannan hanya ta kisan gilla don ciyar da manufar gaban. A 'yan watannin da suka gabata ma dai jaridar Sunday Telegraph ta Birtaniya ta buga wani labara da ke nuni da hannun kungiyar leken asirin cikin kisan gillan da aka yi wa masanan na Iran cikin shekaru biyun da suka gabata. Ko shakka babu abubuwan da wadannan 'yan jarida suka fadi cikin wannan littafi nasu wani abu ne da ke nuni da asalin tushen wannan haramtacciyar kasar wacce ta ginu bisa kisan gilla da ayyukan ta'addanci.
1075084


captcha