Bnagaren kasa da kasa, musulmin kasar Myamnar na cikin kunci da balain rayuwa a sansanin yan gudun hijira da suke inda aka zaunar da su inda suke fuskantar karancin abubuwa na rayuwa kamar kayyayklin kiwon lafiya da suka hada da magunguna da sauransu balanta abinci da ruwan sha mai tsafta.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na gidan talabijin din Press TV, cewa wadanda suka gani da idanunsu sun sheda cewar musulmin kasar Myamnar na cikin kunci da balain rayuwa a sansanin yan gudun hijira da suke inda aka zaunar da su inda suke fuskantar karancin abubuwa na rayuwa kamar kayyayklin kiwon lafiya da suka hada da magunguna da sauransu balanta abinci da ruwan sha mai tsafta da dai sauransu.
Rahotannin sun tabbatar da cewa yan addinin Bouza a Myanmar suna ci gaba da kai hare haren wuce gona da iri kan al'ummar musulmi kasar. Rahotonni daga Myanmar suna bayyana cewa: Har ya zuwa yanzu mabiya addinin Bouza da taimakon jami'an tsaron Myanmar suna ci gaba da kai hare hare kan musulmi a yankin arewa maso yammacin kasar, inda suke kona gidaje da masallatai. Musulmai fiye da 70,000 ne suke rayuwa a garin Sitou da ke lardin Rakhine, amma saboda matsalar hare haren ta'addancin da suke fuskanta daga 'yan Bouza sun tsere daga garin, sauran wadanda suka rage ba su shige 6,000 kacal ba.
Har ila yau rahotonni sun tabbatar da cewa: Musulmai da suke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira na Ruhainghiyon suna fama da matsalar karancin abinci da na magunguna, kuma a cikin kwanaki arba'in kacal da tsugunar da su a wannna sansanin ya zuwa yanzu mutane 18 ne suka rasa rayukansu ciki har da kananan yara.
1076457