IQNA

Wani Sabon Salo Na Kyamar Mabiya Addinin Muslunci A Kamfen zanen Amurka

15:34 - August 13, 2012
Lambar Labari: 2392072
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da zaben Amurka yake ci gaba da karatowa yan takarar neman shugabancin kasar sun kara matsa kaimi wajen nuna tsanin kiyayayrsu da gaba ga addinin muslunci domin yin amfani da hakan wajen samun kuri’ar mutanen kasar da kuma samun goyon bayan yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam, cewa a daidai lokacin da zaben Amurka yake ci gaba da karatowa yan takarar neman shugabancin kasar sun kara matsa kaimi wajen nuna tsanin kiyayayrsu da gaba ga addinin muslunci domin yin amfani da hakan wajen samun kuri’ar mutanen kasar da kuma samun goyon bayan yahudawan sahyuniya wadanda suke rike da wuyan Amurka.
A wani labarin na daban kuma shugaban Kasar Iran Mahmud Ahmadi Nejad na kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya domin halartar taron kasashen musulmi. A yayin da ya ke shirin tafiya a yau litinin, shugaban na jamhuriyar musulunci ta Iran ya ce: "Kungiyar kasashen musulmi tana iya zama wani fagen da gwamnatocin musulmi za su bunkasa gudanar da ayyuka a tsakaninsu." Shugaba Ahamd Nejad ya kara da cewa a halin da ake ciki a yanzu a wannan yankin na gabas ta tsakiya da kuma duniyar musulmi wajibi ne a tuntubi juna, tare da nuna fatansa akan cewa taron da za a yi a birnin makka mai alfarma zai taimaka wajen samar da hadin kai tsakanin al'ummu da gwamnatoci.
Da safiyar yau ne dai shugaban kasar Iran ya kama hanyar zuwa Saudiyya domin halartar taron kungiyar ta kasashen musulmi da za a yi a yau. Sarkin Saudiyya Abdullah Bin Abdulaziz ne dai ya gayyaci shugabannin kasashen musulmi domin yin taron gaggawa a yau litinin da gobe talata domin tattauna matsalolin da musulmi su ke fuskanta.
1076035










captcha