IQNA

Yin Riko Da Koyarwar Kur’ani Shi Ne Sirrin Da Yasa Iran Ta Damu Da Hadin kan Musulmi

23:16 - August 14, 2012
Lambar Labari: 2393159
Bangaren kasa da kasa, a wannan zamani yin riko da koyarwar kur’ani mai tsarki tsakanin al’ummar musulmi shi ne babban abin da zai iya kai wannan al’umma ga samun hadin kai da fahimtar juna da kuma yin watsi da banbancin mazhabibi wanda kuma hakan shi ne ya sanya Iran ta fi kowace kasa damuwa da hadin kan al’ummar musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shi da wani daga cikin masana ya bayyana cewa a wannan zamani yin riko da koyarwar kur’ani mai tsarki tsakanin al’ummar musulmi shi ne babban abin da zai iya kai wannan al’umma ga samun hadin kai da fahimtar juna da kuma yin watsi da banbancin mazhabibi wanda kuma hakan shi ne ya sanya Iran ta fi kowace kasa damuwa da hadin kan al’ummar musulmi kamar yadda kowa yake shedwa a wannan zamani.
A wani labarin na daban kuma jami’ar muslunci ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar za ta fara aiwatar da wani shiri na bayar da dama ga mutane da suke bukatar yin karatu a wannan jami’a daga nesa su yi amfani da hanyar yanar gizo domin yin karatun kamar dai yadda wasu jami’oin suke yi.
A wani bayanin kuma ana shirin gudanar da zaben shugfaban kasar Masar zagaye na biyu tsakanin ‘yantakara biyu na kungiyar Ikhwanul muslimin da kuma Muhammad marsi da kuma mai zaman kansa kuma tsohon pira minista alokacin mulkin kama karya na Husni Mubarak Ahmad Shafiq wadanda dukakninsu suka samu kuri’u fiye da na sauran a zagayen farko.
Masu zabe sun fito a rana ta biyu don zaben shugaban kasa a kasar Masar a yau Alhamis. Duk da cewa wasu suna ganin fitowar masu zaben shugaban kasa a jiya laraba bai kai na zaben yan majalisar dokokin kasar ba. Amma duk da haka fitowar tana da yawa har sai da wasu suka kasa kada kuri'arsu a jiya don yawan masu zabe, don haka ne suka fito a yau don kada kuri'arsu.
1073514























captcha