Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na cikin gida, cewa daya daga cikin malamai kuma mahalarta gasar kur’ani ya bayyana cewa ya zama wajibi a rika mayar da hankali matuka ga bangarorin kur’ani mai tsarki da suke shiryar da dan adam suna yi masa hannunka mai sanda kan rayuwa tare da tarbiyantar da shi a lokacin gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta daliban jami’oin musulmi da ake gudanarwa akowace shekara.
Masana da manazarta za su gudanar da wani taron da aka yi wa take da ranar Ali (AS) a birnin Lkhu na kasar India wanda zai daidai da ranar da ake gudanar da bukukuwa na haihuwar Imam Amirul muminin (AS) a dukkanin kasashen duniya domin raya wannan rana mai albarka.
Malaman addinin muslunci a kasar Iraki sun yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai kan miliyoyin mutanen da suka gudanar da tarukan cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a yankunan kasar Iraki domin kawo cikas ga wadannan taruka.
Miliyoyin mutane ne su ke ci gaba da juyayin zagayowar kwanaki 40 na ashura a birnin Karbala na kasar Iraki, rahotannin da su ke fitowa daga Karbala sun ce ana hasashen cewa mutanen da su ka cika birnin sun haura miliyan 10, da su ka hada mutanen kasar da kuma bakin da su ka zo daga kasashen makwabta.
Miliyoyin Irakawa ne dai su ka ti tattaki da kafafunsu daga garuruwa masu nisa domin zuwa karbala.
A gefe daya 'yan ta'adda sun rika kai hare-gare ga masu tafiyar zuwa karbala sai dai hakan bai hana mutane ci gaba da azamar isa hurumin imam Hussain (a.s.) ba, a yau ma mutane 20 ne su ka yi shahada saboda harin da wani dan kunar bakin wake ya kai musu a garin Basra.
1078726