IQNA

An Yi Kira Zuwa Ga Gudanar Da Babban Taron Khatmar Kur’ani A Dandalin Tahrir

17:37 - August 17, 2012
Lambar Labari: 2395000
Bangaren kasa da kasa, an yi kira zuwa ga wani babban taro a dandalin tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira na kasar Masar domin karatun kur’ani mai tsarki a ranar juma’a ta karshen watan ramadan mai alfarma kamar dai yadda masu shirya taron na kungiyar ikhwan suka fada.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar misriyun, cewa an yi kira zuwa ga wani babban taro a dandalin tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira na kasar Masar domin karatun kur’ani mai tsarki a ranar juma’a ta karshen watan ramadan mai alfarma kamar dai yadda masu shirya taron na kungiyar ikhwan suka fada ga manema labarai.
marubucin kasar Masar Ala Aswani ya ce mika mulkin kasar Masar ga hannun Ahmad shafiq tsohon pita ministan kasar lokacin mulkin tsohon shugaban mulkin kama karya Husni Mubarak hakan na nufin cewa juyin juya halin da al’ummar kasar suka yi ya kawo karseh kenan domin wadanda aka kawar sun dawo.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.
Tafiyar da Ali Juma’a ya yi zuwa birnin Qods ya yi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta haramatcciyar kasar Isra’ila wanda kuma ko shakka babu hakan ya sanya gagarumin shakku a cikin zukatan mutanen kasar dangane da wannan ziyara tasa, duk kuwa da cewa daga cikin abubuwan da ya yi har da duba lafiyarsa a asibiti.
Yan majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba.
1079459



















captcha