Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin malaman addinin muslunci a kasar Lebanon ya bayyana cewa, batun masallacin Qods mai alfarma batu na sasi a cikin manyan rukunnai na addini msulunci domin kuwa masallacin shi ne alkiblar farko ta addinin muslunci kafin dakin Ka’abah.
Kamfanin dilllancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa Sheikh Abu Ardat daya daga cikin malaman addinin muslunci a kasar Lebanon ya bayyana cewa, batun masallacin Qods mai alfarma batu na sasi a cikin manyan rukunnai na addini msulunci domin kuwa masallacin shi ne alkiblar farko ta addinin muslunci kafin dakin Ka’abah kamar dai yadda ya tabbata a cikin kur’ani mai tsarki.
Mansur Marzuki shugaban kasar Tunisia ya yi dirar mikiya kan masu akidar salafiya na kasar da cewa suna mayar da hannun agogo baya a cikin dukaknin harkoki na siyasa a kasar tare da yada tunaninsu na neman tashin hankali da kawo fitina a cikin al’ummar musulmi kamar yadda ake gani a duk inda suka wata kungiya ko cibiya, a cikin kasashen musulmi da ma kasashen da ba na musulmi ba.
Ya ci gaba da cewa dle ne a dauki dukaknin matakan da suka dace domin takawa ‘yan salafiyya burki kan ayyukansu na wuce gona da iri, tare da kara fadakar da mutane kan muhimmancin zaman lafiya da kuma kaurace ma su neman fitina acikin al’ummar musulmi, wanda a cewarsa hakan ne kawai zai kawo zaman lafiya a cikin al’umma.
Masur Marzuki shugaban kasar Tunisia ya yi dirar mikiya kan masu akidar salafiya na kasar da cewa suna mayar da hannun agogo baya a cikin dukaknin harkoki na siyasa a kasar tare da yada tunaninsu na neman tashin hankali da kawo fitina a cikin al’ummar musulmi, domin kawai su cimma manufofinsu.
1080769