IQNA

An Bude Tashar Muslunci Ta Farko A Kasar Rasha Da Nufin Bayyana Hakikanin Muslunci

22:12 - August 21, 2012
Lambar Labari: 2396724
Bangaren kasa da kasa, a karon farko an bude wata tashar talabijin ta muslunci a kasar Rasha a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan idin karamar salla na wannan shekara da nufin bayyana wa mutanen kasar hakikanin addinin muslunci da kuma ilmantar da su kansu musulmi su san addininsu.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Imarat yaum, cewa a karon farko an bude wata tashar talabijin ta muslunci a kasar Rasha a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan idin karamar salla na wannan shekara da nufin bayyana wa mutanen kasar hakikanin addinin muslunci da kuma ilmantar da su kansu musulmi su san addininsu maimakon bin tafarkinsa ba tare da ilimi ba.
Shugaban majalisar dokokin kasar Masar Hamad Sa’ad ya mayar da da sakon taya murna da majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aike masa tare da bayyana cewa ba su yin na’am da duk wani sakon taya murna daga wannan haramtacciyar kasa da ke dasawa da tsohuwar gwamnatin kama karya.
A bangare guda kuma ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-ra’ay ta kasar Masar cewa, wahabiyawan kasar Masar sun kawafa wani kwamiti na umurni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna wanda da dama daga cikin al’ummar kasar suka yi Allawadai da shi kamar yadda ita ma jami’ar Azhar kan kafa wannan kwamiti domin aiwatar da manufar wata kasa da ke bin akidar wahabiyanci da ke yankin.
Al’ummar kasar Masar dai suna zargin gwamnatin kasar saudiyya da hannu kai tsaye wajen taimaka wa ‘yan salafiyya da ke bin akidar wahabiyanci, kuma abin da yake faruwa yanzu haka a kasar ya tabbatar da wannan aniya ta wahabiyawan.
1082371




















captcha