IQNA

Tura Wata Tawaga Ta Masu Bayar da Agaji Na Sa kai Daga Malazia Zuwa Myanmar

22:12 - August 21, 2012
Lambar Labari: 2396726
Bangaren kasa da kasa, a cikin mako mai zuwa ne ake sa za a tura wata tawagar masu bayar da agaji daga kasar Malazia zuwa kasar Myanmar domin taimakon musulmin da ake zalunta tare da raba su da rayuwarsu da mahallancu da dukiyoyinsu saboda tsabar zalunci da danniya.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na the star, cewa a cikin mako mai zuwa ne ake sa za a tura wata tawagar masu bayar da agaji daga kasar Malazia zuwa kasar Myanmar domin taimakon musulmin da ake zalunta tare da raba su da rayuwarsu da mahallancu da dukiyoyinsu saboda tsabar zalunci da danniya tare da sanin halin da suke ciki.
A wani rahoton kuma daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Lebanon ta Al-intiqad cewa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
Kungiyar ta kasar Lebanon ba ya ga kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar, ta kirayi iriin wadannan manafukan larabawa da su sake yin nazari kan makomarsu bisa la’akari da halin da ake ciki yanzu haka a yankin.
1081685






















captcha