IQNA

Italia Za Ta Dauki Nauyin Taro Na Kasa Da Kasa Mai Taken Allah Hasken sama Da Kasa

22:46 - August 25, 2012
Lambar Labari: 2398480
Bangaren kasa da kasa, za a shirya gudanar da wani taron addini a kasar Italia tare da halartar masana da kuma malaman addinin daga sssa na kasar da ma wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa domin kara fadakar da musulmin kasar da ma wadanda ba musulmi hakikanin koyarwar addini ta zaman lafiya tare da sauran addinai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam online, cewa za a shirya gudanar da wani taron addini a kasar Italia tare da halartar masana da kuma malaman addinin daga sssa na kasar da ma wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa domin kara fadakar da musulmin kasar da ma wadanda ba musulmi hakikanin koyarwar addini ta zaman lafiya tare da sauran addinai kamar dai yadda yake acikin koyarwar muslunci.
A wata wasika da ya aikewa Majalisar Dokokin kasar a jiya, shugaban kasar Tunisiya Moncef Marzuki ya ce kokarin da magoya bayan jam'iyyarsa ta Annahda ke yi na ganin cewa sun yi kane-kane a kan madafan iko na kasar ba tare da bai wa sauran jam'iyyu damar shiga a dama da su ba, abu ne da zai iya kawo wa jinjirar dimokuradiyyar kasar koma-baya. A cikin wasikar wadda wani mai ba shi shawara ya karanta a cikin zauren Majalisar amadadinsa, shugaba Marzuki ya fito fili karara inda ya nuna yatsa a kan wasu magoya bayan jam'iyyarsa ta Annahda kan cewa suna kokarin kame dukkanin madafan iko na kasar alhali kuwa Tunisiya kasa ce da ke kunshe da mutane masu bambancin ra'ayoyi.
To sai dai a lokacin da ake karanta wannan wasika, da dama daga cikin 'yayan jami'iyyar ta Annahda da suka hada da ministan kare hakkokin bil'adama Samir Dilou da kuma na ma'aikatar cikin gida Ali Larayedh sun fice daga cikin zauren Majalisar domin nuna fushinsu a game da wadannan kalamai na shugaba Moncef Marzuki.
1083146





captcha