Bangaen kasa da kasa, an bude wani babban baje koli mai taken muslunci a kasar Rasha a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar da nufin nuna irin gagarumin ci gaban da addinin muslunci yake samua kasar rasha wanda hakan sakamako ne na gagarumin aikin da malaman addini suke yi a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Rasha a yau, cewa an bude wani babban baje koli mai taken muslunci a kasar Rasha a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar da nufin nuna irin gagarumin ci gaban da addinin muslunci yake samua kasar rasha wanda hakan sakamako ne na gagarumin aikin da malaman addini suke yi a kasar, wadda akasarin mutanenta kirisroci ne.
Yanzu haka dai ana shirin gudanar da wata gasa kan muhimman abubuwan da addinin muslunci ya ginu a kansu wadda ta kebanci matasa mabiya addinin muslunci na kasar wadda za ta gudana a birnin Rayazan na kasar tare da halartar malaman addini da kuma masana da shugabannin cibiyoyi.
Bayanin ya ce an bude wani masallaci a cikin bababr hedikwatar ‘yan sanda da ke birnin Bankok fadar mulkin kasar Thailand a wani mataki na kara tabbatar da mabiya addnin muslunci da ke kasar a matsayin daya daga cikin mabiya addinai sannu a kasar wadda akasarin mabiya addinain buda.
1083710