IQNA

Shugabar Kasar Myanmar Ta Taya Musulmin Kasar Bakin Cikin Abin Da Ya Faru

11:21 - August 26, 2012
Lambar Labari: 2398920
Bangaren kasa da kasa, shugabar kasar Myanmar ta taya musulmin kasar bakin cikin abin day a faru na kisan kiyashin da aka yi msuu babu gaira babu sabar a cikin watannin da suka gabata wanda hakan ya zubar da mutuncin kasar baki daya a idon duniya tare da jawo mata yin kakakusar suka da allawadai.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar radio ta Faransa, cewa shugabar kasar Myanmar ta taya musulmin kasar bakin cikin abin da ya faru na kisan kiyashin da aka yi msuu babu gaira babu sabar a cikin watannin da suka gabata wanda hakan ya zubar da mutuncin kasar baki daya a idon duniya tare da jawo mata yin kakakusar suka da allawadai kan wannan mummunan aiki.

A cikin watannin bayan nan, musulmin kasar Mayammar sun zama karen gwajin dafi na nuna kin jiki da tsangwana. Mabiya addinin Budda masu tsattsauran ra'ayi a yankin Rakhtin da ke yammacin kasar suna yi wa musulmin kisan gilla saboda kawai su musulmi ne. Ita kuwa gwamnatin kasar ta sanya ido tana kallon abinda ya ke faruwa ba tare da dauki matakin da ya dace ba. Har ila yau, kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama a duniya sun yi gum da bakunansu kai kace wadanda ake kashewa ba bil'adama ba ne da su ke riya cewa suna karewa hakki. Kawo ya zuwa yanzu lamirin duniya bai girgiza ba akan kisan da ake yi wa musulmin mayyamar da kona gidajensu da shagunansu na kasuwanci.

Babu wanda ya zubar da koda hawaye akan musulmi dubu dari takwas da rayuwarsu ta ke fuskantar bakar wahala. Shin saboda mutanen da ake kashewa a muyammar musulmi ne, ko kuma saboda tsiraru ne? Yadda al'amurra su ke tafiya a cikin kasar ta Muyammar a yanzu na nuni da cewa za a ci gaba da samun asarar rayuka anan gaba, tunda dai babu alamar za a takawa masu makasa birki. Ga dukkanin alamu'kisan da 'yan budda su ke yi wa musulmi a cikin Muyammar suna yi ne da tallafin gwamnatin kasar. Su ke kuma korarsu daga gidajensu da maida su zama 'yan gudun hijira na tilas. A tsammani shi ne addinin Budda wanda ya yi imani da halin kirki da kyautatawa halittu, da s u ke kira Neravana, su zama masu kyautatawa abokan zama da su.

A lokacin da 'yan taliban su ka tarwatsa gumakan Budda a Afgahnistan , wadannan musulmin da ake kashe wa a yanzu sun yi Allah wadai da Taliban su ka kuma bayyana abinda su ka yi da cewa keta ce da mugunta. Daruruwan shekaru musulmin kasar Thalidan su ka yi suna rayuwa da mabiya addinin Budda, amma ana samun sauyin siyaya a cikin kasar sai abokan zamansu su ka ci amanarsu da fara kashe su. Da gangan ake son nuna cewa a duk inda musulmi su ke a duniya masu son tada hankali ne. Wannan siyasa ce yammacin turai ke amfani da ita a lokaci mai tsawo.

Wannan kuwa ba shi ne karon farko ba da aka yi wa musulmin mayammar kisan kiyashi. A tsawon lokacin mulkin sojan wannan kasa sun zama zakaran gwajin dafi na nuna kiyayya a gare su. Abin da ake sa ran kungiyoyin kasa da kasa su aikata shi ne kawo karshen wannan irin kisan da ake yi wa musulmin muyammar, saboda su ma su rayu daidai da kowace al'umma a duniya.
1084099





captcha