Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Masar sun yanke shawar bude mashigar Rafah da ta hada kasar da kuma yankin zirin Gaza domin bayar da dama ga dubban palastinawa su yi shige da fice tsakanin yankunan biyu ba tare da wata wahala ba kamar dai yadda bangaren kula da iyakokin kasar ya sanar a jiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI, cewa mahukuntan kasar Masar sun yanke shawar bude mashigar Rafah da ta hada kasar da kuma yankin zirin Gaza domin bayar da dama ga dubban palastinawa su yi shige da fice tsakanin yankunan biyu ba tare da wata wahala ba kamar dai yadda bangaren kula da iyakokin kasar ya sanar a jiya lahadi.
Ita kuwa kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta yi suka kan furucin da ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra'ila ya yi kan shugaban hukumar Palasdinawa. A bayanin da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta fitar a yau lahadi ta bayyana cewar furucin da ya fito daga bakin ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra'ila Avigdor Lieberman kan shugaban hukumar cin gashin kan Palasdinawa Mahmud Abbas Abu-Mazin furuci ne da ke nuni da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila bata san abin da take yi ba.
Sakamakon haka kungiyar ta Larabawa zata ci gaba da goyon bayan al'ummar Palasdinu, tare da fuskantar bakar siyasar gwamnatin h.k.Isra'ila da ta yi hannun riga da dokokin kasa da kasa, har sai ta mika kai ga bukatar kungiyoyin kasa da kasa da ke neman wanzar da zaman lafiya da sulhu masu daurewa a yankin gabas ta tsakiya ta hanyar kafa 'yantacciyar kasar Palasdinu.
Shi kuwa ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila dai ya yi dirar mikiya ce kan shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas kan bukatar da ya gabatar na neman bai wa hukumar Palasdinawa kujera da ba ta dindindin ba a Majalisar Dinkin Duniya, sannan ya bayyana rashin amincewar majalisar ministocin h.k.Isra'ila da duk wani zaman tattaunawa da Palasdinawa gami da daukan matakin hana Mahmud Abbas komawa ga Majalisar Dinkin Duniya don neman amincewarta kan kafa kasar Palasdinu a kan iyakar da aka shata a shekara ta alif dari tara da saba’in da bakwai.
1084923