IQNA

An Girmama wasu Daga Cikin palastinawa Da Suka Nuna Kwazo A Gasar Kur’ani

18:00 - August 27, 2012
Lambar Labari: 2400215
Bangaren kasa da kasa, an giramam wasu daga cikin palastinawa da suka nuna kwazo a yankin Ramallah inda al aba su kyatuka da suka hada da kudade da littafai daidai da matakin da suka taka a lokacin gudanar da gasar tare da halartar wakilan ciboyin addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ma’a, cewa an giramam wasu daga cikin palastinawa da suka nuna kwazo a yankin Ramallah inda al aba su kyatuka da suka hada da kudade da littafai daidai da matakin da suka taka a lokacin gudanar da gasar tare da halartar wakilan ciboyin addini muslunci.
Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta yi suka kan furucin da ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra'ila ya yi kan shugaban hukumar Palasdinawa. A bayanin da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta fitar a yau lahadi ta bayyana cewar furucin da ya fito daga bakin ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra'ila Avigdor Lieberman kan shugaban hukumar cin gashin kan Palasdinawa Mahmud Abbas Abu-Mazin furuci ne da ke nuni da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila bata san abin da take yi ba.
Sakamakon haka kungiyar ta Larabawa zata ci gaba da goyon bayan al'ummar Palasdinu, tare da fuskantar bakar siyasar gwamnatin h.k.Isra'ila da ta yi hannun riga da dokokin kasa da kasa, har sai ta mika kai ga bukatar kungiyoyin kasa da kasa da ke neman wanzar da zaman lafiya da sulhu masu daurewa a yankin gabas ta tsakiya ta hanyar kafa 'yantacciyar kasar Palasdinu.
Avigdor Lieberman dai ya yi dirar mikiya ce kan shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas kan bukatar da ya gabatar na neman bai wa hukumar Palasdinawa kujera da ba ta dindindin ba a Majalisar Dinkin Duniya, sannan ya bayyana rashin amincewar majalisar ministocin h.k.Isra'ila da duk wani zaman tattaunawa da Palasdinawa gami da daukan matakin hana Mahmud Abbas komawa ga Majalisar Dinkin Duniya.
1084898

captcha