Bangaren kasa da kasa, an bayyana kasashen yan ba da cewa kasashe ne ya kamata a ce ba su karkata zuwa matsin lamabar wasu daga manyan kasashe da suke yin amfani da karfi wajen danne sauran kasashen duniya wanda hakan ko shakka babu yana da muhimmanci ga makomarsu a nan gaba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakato daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na cikin gida, cewa an bayyana kasashen yan ba da cewa kasashe ne ya kamata a ce ba su karkata zuwa matsin lamabar wasu daga manyan kasashe da suke yin amfani da karfi wajen danne sauran kasashen duniya wanda hakan ko shakka babu yana da muhimmanci ga makomarsu a nan gaba a siyasance.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Ramin-Mihman Perast ya ce ministocin harkokin waje na kasashen duniya akalla 80 ne aka tabbatar da cewa za su halarcitaron share fage da ministocin harkokin wajen wannan Kungiya ta 'Yan Ba-ruwanmu da zai gudana a gobe talata da kuma jibi laraba a nan Tehran. Tuni dai ministoci daga kasashe daban-daban na duniya wadanda mambobi ne a wannan kungiya suka soma isowa a nan birnin Tehran, daga cikin wadanda suka iso kuwa har da ministan harkokin wajen kasar Kuweiti Mohammad Al-Sabah da kuma takwaransa na kasar Bahrain Khalid Bin Ahmad Ali-Khalifa wadanda yanzu haka suna a nan birnin Tehran.
Wannan taron shuwagabannin kasashen kungiyar zai gudana ne a ranakun 30 da kuma 31 ga wannan wata na Agusta a nan Tehran, kuma za a samu halartar shuwagabannin kasashe, da na gwamnatoci da kuma wakilai daga kasashe 120 mambobi a kungiyar wacce aka kafa a shekara ta 1961 domin karfafa 'yancin da kasashen duniya suke da shi da kuma kasancewa 'yan ba-ruwanmu a game da salon siyasar kasashen nan biyu da ke nuna isa a wancan lokaci wato Amurka da kuma Tarayyar Soviet a wancan lokaci.
1086713