IQNA

Wahabiyawan Pakistan Sun Nuwa Wani Hoto yadda Suka Fille Kawunan Wasu Mutane Biyu

22:23 - August 29, 2012
Lambar Labari: 2401568
Bangaren kasa da kasa, wahabiyawan kasar Pakistan sun nuna wani hoton bidiyo da ke nuna yadda suka fille kawunan wasu mutane biyu mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah lamarin ya daga hankulan al’ummar musulmi na kasar inda suka yi kira da a dauki matakai na ladabtar da wahabiyawa masu aikata wannan ta’addanci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV, cewa wahabiyawan kasar Pakistan sun nuna wani hoton bidiyo da ke nuna yadda suka fille kawunan wasu mutane biyu mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah lamarin ya daga hankulan al’ummar musulmi na kasar inda suka yi kira da a dauki matakai na ladabtar da wahabiyawa masu aikata wannan ta’addanci kan musulmi.
A bangare guda kuma ana shirin fara gudanar da wani zaman taro kan matsayin kur’ani mai tsarki da kuma limaman iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kasar Pakistan wanda zai gudana agarin Binjaba da ke kasar, kamar yadda aka saba gudanarwa lokaci zuwa lokaci.
Ana sake gina wa mabiyar tafarkin iyalan gidan manzon Allah masallatansu da ‘yan ta’adda suka rusa a yankuna daban-daban na kasar Pakistan wanda ciyar Amal ta kasar da kuma cibiyar Imam Hussain ta kasar Kuwait suka dauki nauyin ginawa a yankuna uku na kasar da suka hada Benjab.
An bayar da lasisi ga kungiyoyin addinin muslunci kimanin arba’in da bakwai 47 domin gudanar da ayyuaknsu cikin izini a kasar Tajikistan kamar dai yadda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar.
1086866






















captcha