IQNA

Hakurin Da Al’ummomin Duniya Suke Kan Zaluncin Manyan kasashe Ya Fara Kawo Karshe

17:44 - August 30, 2012
Lambar Labari: 2401827
Bangaren siyasa, hakurin da al’ummomin duniya suke yi kan zalunci da danniyar manyan kasashe masu zalunci ya fara kawo karshe kuma mikewar da wadannan al’ummomi suke yi ta zama babban dalili da ke tabbatar da hakan domin kuwa sun gane cewa ba demokreadiyya ce ta dami yan mulkin mallaka ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagoran juyin juya halin muslunci cewa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa hakurin da al’ummomin duniya suke yi kan zalunci da danniyar manyan kasashe masu zalunci ya fara kawo karshe kuma mikewar da wadannan al’ummomi suke yi ta zama babban dalili da ke tabbatar da hakan domin kuwa sun gane cewa ba demokreadiyya ce ta dami yan mulkin mallaka ba ko hakkokin sauran al’ummomi.
A yau ne jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Aytaollah Sayyid Ali Khamenei ya bude babban taron shugabannin kungiyar kasashen ‘yan baruwanmu a birnin Tehran.
A lokacin da yake gabatar da jawabin bude zaman taron, jagoran juyin juya halin yay i ishara da muhimmancin da wannn kungiya take da shi a matsayin siiasa ta duniya, da kuma rawar da take takawa a matsayi na kasa da kasa, kasantuwar mambobin kungiyar su ne kashi biyu bisa uku na dukkanin kasashen duniya, inda ya ce za su samar da wani canji da zai daidaita siyasar da duniya take tafiya a kanta ta rashin adalci, inda wasu ‘yan tsirarun kasashe na yammacin turai suke juya duniya yadda suke so a siyasance da kuma fuskar tattalin arziki har ma da lamrin tsaro.
A wani bangaren bayanin nasa kuma kuma ya caccaki kasar Amurka dangane da da’awar da take yi kan hana yaduwar makaman nukiliya, inda ya ce Amurka ce kasar da take mallakar dubban kawunan nukiliya, kuma ita ce kasa daya tilo a duniya da ta yi amfani da makaman nukiliya kan bil adama, kuma har yanzu tana ci gaba da kera irin wadannan makamai masu barazana rayuwar bil adama a bayansa.
Ya ce abin mamaki ne yadda wanna kasa a lokaci guda take matsin lamba kan Iran bisa zargin cewa Iran din za ta iya kera makaman nukiliya a shirin da take gudanarwa na ayyukan farar hula, ya ce Iran ba ta da niyar kera makaman nukiliya kuma duniya ta tabbatar da hakan, amma kuma alokaci za ta ci gaba da shirinta domin ayyuka na farar hula.
Dangane da sha’anin palstinu kuwa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa al’ummar Palastine sun kwashe tsawon shekaru sama da sittin suna fama da matsalolin da yahudawan Sahyuniya suka jefa su a cikin yankunansu, yayin da wasu miliyoyi kuma aka raba da mahallansu aka mayar da su yan gudun hijira, kuma abin takaici kasashen da suke iko da siyasar duniya suna kiran palastinawa masu neman hakkokinsu a matsayin ‘yan ta’adda.
Jagoran ya jadda cewa kasashen kungiyar suna da nauyi da ya rataya kansu, shi ne tabbatar da adalci a cikin siyasar kasa da kasa, tare da hada karfi da karfe domin kawo karshen babakeren manyan kasashe yan mulkin mallaka kan sauran al’ummomin duniya.
1088072



captcha