IQNA

Rashin Adalci Ne Ya Kawo Rashin Amincewar Kasashe Ga Manyan ‘yan mulkin Mallaka

17:43 - August 30, 2012
Lambar Labari: 2401828
Bangaren siyasa, rashin adalcin da duniya take gani shi ne abbabn dalilin da ya sanya sauran al’ummomi bas u amince da manayna kasashen duniya yan mulkin mallaka ba domin ya tabbata cewa masu da’awar kare hakkin dan adam da demokradiyya su ne kan gaba wajen karya hakkokin mutanen duniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada abaransa, cewa rashin adalcin da duniya take gani shi ne abbabn dalilin da ya sanya sauran al’ummomi bas u amince da manayna kasashen duniya yan mulkin mallaka ba domin ya tabbata cewa masu da’awar kare hakkin dan adam da demokradiyya su ne kan gaba wajen karya hakkokin mutanen duniya da rusa demokradiyya din.
Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya karbi ragamar shugabancin kungiyar ‘yan baruwanmu a hukumance daga hannun shugaban kasar Masar Muhammad Mursi a lokacin bude babban taron shugabannin kasashe mambobi a kungiyar a yau a nan birnin Tehran.
A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa, shugaba Ahmadinejad ya bayyana cewa, lokaci ya yi da kasashe 120 mambobi a kungiyar za su kawo sabon sauyi a cikin siyasar duniya, kasantuwar cewa majalisar dinkin duniya ta rasa matsayinta wanda aka kafa ta saboda shi, wato kiyaye hakkokin al’ummomin duniya tare da tabbatar da adalci a tsakaninsu, inda ya ce yanzu majalisar ta zama tamkar kayan wasa a hannun wasu yan tsirarun manyan kasashen duniya, da suke yin amfani da ita wajen cimma manufofinsu na siyasa kan sauran al’ummomin duniya, inda ya ce kungiyar ‘yan baruwanmu za ta iya taka gagagrumar rawa wajen taka wa kasashe masu girman kai birki, tare da dawo ma sauran al’ummomin da yancinsu na siyasa da zamantakewa da tattalin arzikinsu, maimakon bin tsari da jari hujja da aka dankara kansu.
A nasa bangaren shugaban kasar Masar bayan ya mika ragamar jagorancin kungiyar ga shugaba Ahmadinejad, ya yi wa Iran fatan dacewa wajen gudanar da jagorancin kungiyar, wanda zai kai ga ci gaban da dukkanin mambobinta suke tsammani daga kasar ta Iran.
1088027

















captcha