Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa h.k. Isra'ila hatsari ne mai girma ga kasashen yankin gabas ta tsakiya saboda makaman Nukiliyar da ta mallaka. A yayin da ya jagoran juyin musuluncin ya ke ganawa da babban magatakardar majalisar dinkin duniya Bon Ki Moon.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shfin sadarwa na ofishin jagoran juyin juya hali cewa, jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa h.k. Isra'ila hatsari ne mai girma ga kasashen yankin gabas ta tsakiya saboda makaman Nukiliyar da ta mallaka. A yayin da ya jagoran juyin musuluncin ya ke ganawa da babban magatakardar majalisar dinkin duniya Bon Ki Moon, ya yi ishara da yadda Amerika ta ke bada muggan makamai ga h.k. Isra'ila sannan ya kara da cewa.
Wannan wani lamari ne mai hatsarin gaske ga wannan yankin, kuma abin da ake tsammani daga m.d.d. shi ne daukar mataki akan hakan." Jagoran juyin musuluncin ya kuma yi ishara da damuwar a dukkanin bil'adama su ke yi tarayya akanta dangane da makaman nukiliya sannan ya kara da cewa: " Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana nanata wajabcin kawar da makaman nukiliya daga yankin gabas ta tsakiya." Sa dai jagoran ya bayyana takaicinsa akan matsalar da m.d.d ta ke da shi, saboda yadda kasashe masu takama da karfi wadanda kuma su ka taba amfani da makanin nukiliya su ked a iko akan kwamitin tsaro na .d.d.
Dangane da kasar Syria kuwa jagoran ya fadawa Bon Ki Moon cewa; makaman da ake aikewa ta kan iyakoki zuwa kasar ta Syria da su ke shiga hannun kungiyoyi daban-daban su ne matsala. Har ila yau jagoran ya ce; gaskiya mai daci dangane da kasar Syria ita ce, kungiyoyin da su ke dauke da makamai suna yi yaki ne na wakilci.
1087870