IQNA

Kafofin Yada Labarai Za Su Iya Taka Rawa Mai kyau A Fagen Siyasar Duniya

21:59 - August 31, 2012
Lambar Labari: 2402205
Bangaren siyasa, kafafen yada labarai za su iya taka gagarumar rawa adukkanin bangarori na siyasar duniya musamman wannan lokacin da ya zama kafofin yada labaran turai musamman na yin amfani da wannan damar domin kare bakaken mabufofin siyasa na kasashensu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a lokacin da yake zantawa da pira ministar kasar Sri Lanka, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya jaddada cewa, kafafen yada labarai za su iya taka gagarumar rawa adukkanin bangarori na siyasar duniya musamman wannan lokacin da ya zama kafofin yada labaran turai musamman na yin amfani da wannan damar domin kare bakaken mabufofin siyasa na kasashensu a kan sauran al’ummomi.
jagoran juyin juya cewa, Kasar Iran na gamsuwa da yanda matsayi da karfi da darajar kasar Iraki, ke bunkasa yau da gobe a cikin duniyar larabawa da musulmi, inji jagoran juyin juya halin musulumci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, yayi wannan furuci ne jiya litinin yayin da ya gana da praministan kasar ta Iraki Nuri Almaliki, da ya kawo wata ziyara a nan Teheran.
Ya kara da cewa, kokarin da zai taimaka wajen kara tabbatar da karfin magabatan kasar ta Iraki, musamman game da jihadi na kimiya hade da ayukan sake gina kasar, sune za su habbaka matsayin kasar da cimma guri da bukatun al'ummar kasar da ma gwamnatin kasar baki daya. Inda ya nuna cewar irin abubuwan da suka gudana a cikin kasar a yan watannin nan, sun farkar da gwamnati da al'ummar kasar game da irin matsayi da kuma rawar da za su iya takawa a cikin duniyar larabawa da musulmi.
A mahangar jagoran juyyin juyya halin musulumci, fucewar daukacin sojojin kasar Amurka daga kasar Iraki na daga cikin manyan abubuwa masu mahimmanci da suka ja hankali kuma wanda aka yi galaba kansu, da suka biyo bayan namijin kokari da kishin kasar da jama'ar kasar Iraki suka nuna, Sannan, karbar bakoncin taron kungiyar hadin kan larabawa da kasar ta Iraki ta yi ya kara nuna karfin gwamnatin kasar.
1088516

captcha