IQNA

Bincike Kan Makomar Imam Musa Sadr Yana Daga Cikin Abin Da Gwamnatin Lebanon Ke Yi

17:57 - September 02, 2012
Lambar Labari: 2403541
Bangaren kasa da kasa, gudanar da bincike kan makomar Imam Muysa Sadr yana daga cikin muhimman lamurra da gwamnatin kasar Lebanon ta mayar da hankali kansu a halin yanzu tare da abokian tafiyarsa biyu wadanda suka bata a kasar Libya tun bayan da tsohon shugaban kasar ya gayyace su.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na Lorient cewa, shugaban kasar Lebanon Michil Sulmain ya sheda cewa gudanar da bincike kan makomar Imam Muysa Sadr yana daga cikin muhimman lamurra da gwamnatin kasar Lebanon ta mayar da hankali kansu a halin yanzu tare da abokian tafiyarsa biyu wadanda suka bata a kasar Libya tun bayan da tsohon shugaban kasar ya gayyace su kimanin shekaru talatin da biyar da suka gabata.
Bayanin ya ci gaba da cewa hakika zaman taron ya yi nasara, muhimamn abubuwa da taron ya mayar da hankali a kansu dais hi ne batutuwa na samar da zaman lafiya, ayyukan na ci gaba, haka nan kuma kasashe mambobi su yi aiki kafada da kafada wajen bunkasa ayyuka na jin kai, kusan dukkanin mambobin kungiyar kashen yan ba ruwanmu sun amince kan samar da hanyoyi na wanzar da zaman lafiya, kawar da talauci a tsakanin al’ummomin kasashen, tare da kyautata rayuwar jama’a.
Ko shakka babu kungiyar kasashen yan ba ruwanmu za ta iya taka gagarumar rawa wajen aiwatar muhimman lamurra a mataki na siyasar duniya, kamar yadda za ta iya taka rawa a bangarori na tattalin arziki da tsaro, domin kuwa kasashen da suke cikin wannan kungiya a matsayin mambobi ya sanya ta zama kungiya mafi girma aduniya bayan MDD, kasantuwar kashi biyu bisa uku na kasashen mambobi ne acikin wannan kungiya, kuma ya zuwa yanzu ta yi rawar gani a bangarori daban-daban wanda duniya ta yaba hakan, musamman bangarorin karfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin da bunkasa harkoki cinikayya da dai sauransu.
1088826



















captcha