Kmafanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo na Bernama cewa, nan ba da jimawa ba za a gudanar da wani zama kan harkokin tatatlin arzikin muslunci a kasar Malzia tare da halartar masana daga sasas da dama da na kasashen yankin inda za su batar da jawabawai da kuma makalolin da suka rubuta kan hakan kamar dai yadda bayanin yay i nuni da aka fitar a jiya.
A wani bayanin kuma Dubban mutane sun gudanar da zan-zanga a birnin Antakiya na kasar Turkiya domin yin Allawadai da gwamnatin kasar kan rawar da take takawa wajen kara iza wutar rikicin kasar Syria tare da baiwa ‘yan alkaida damar shiga kasar Turkiya domin su ketara iyakar kasar zuwa Syria.
Kamfanin dillancin labaran Anadol na kasar Turkiya ya ta babatar da cewa, masu zanga-zangar sun yi cincirindo a gaban babban ginin gwamnatin jahar Hatai, tare da halartar kungiyoyin kwadago da lauyoyi gami da wasu manyan ‘yan kasuwa, inda suka yi ta rera taken yin Allawadai da gwamnatin Rajab Tayyib Ardugan, sakamakon bin sahun Amurka da Isra’ila da ‘yan koransu daga cikin shugabannin larabawa ta da yi wajen haddasa a rikici a cikin kasar Syria, tare da taimaka ma ‘yan ta’adda da mafaka da kuma muggan makamai da suke kashe mutane da su a Syria.
Daya daga cikin jagororin kungiyar Alkaida a kasar Yeman ya fitar da wata yarjejeniyar sirri da suka cimmawa tare da Amurka da gwamnatin Saudiyya, kan kwashe mayakan alkaida daga kasar Yeman zuwa Turkiya, inda za a ba su horo na yaki, daga nan kuma a tur su cikin Syria domin kai hare-hare da sunan yunkurin kawar da Bashar Asad daga mulki.
1088895