IQNA

Harin Ta’addanci Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Fararen Hula ‘Yan Shi’a Bakwai A Pakistan

21:57 - September 02, 2012
Lambar Labari: 2403594
Bangaren kasa da kasa, harin ta’addanci ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla bakwai dukkanin fararen hula mabiya tafarkiniyalan gidan manzon Allah a kasar Pakistan wanda masu akidar kafirta sauran msuulmi suka kai a garin Hizarah a jahar Balochestan ta cikin Pakistan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na levit, cewa harin ta’addanci ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla bakwai dukkanin fararen hula mabiya tafarkiniyalan gidan manzon Allah a kasar Pakistan wanda masu akidar kafirta sauran msuulmi suka kai a garin Hizarah a jahar Balochestan ta cikin kasar.
Al’ummar birnin Mambai na kasar India sun gudanar da wata gagarumar zanga-zangar la’antar gwamatin Amurka da salon siyasarta kan al’ummomin uniya raunana da masu tasowa ta yadda suka bayyana Amurka da cewa ita bababr azzaluma da ke haddasa dukkanin matsaloli a duniya tare da saka kowa cikin matsaloli.
A yayin da ya ke gabatar da jawabinsa a lokacin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana yunkurin al'ummomin kasashen musulmi na kifar da shugabannin kama-karya ‘yan amshin shatan manyan kasashen duniya a matsayin lamari mai matukar muhimmanci sannan kuma wani mafari na yunkurin ganin bayan lalatattun cibiyoyin yahudawan sahyoniya da ma'abota girman kan duniya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Sakamakon wannan yunkuri mai cike da albarka, da yardar Allah al'ummar musulmi za su sake dawo da daukaka, ‘yanci da kuma tsayin dakan da suke shi a baya.
Ayatullah Khamenei ya bayyana matasan kasashen musulmin a matsayin masu dauke da babbar bishara ga makomar al'ummar musulmi, daga nan sai ya ce: Farkawar da matasan kasashen musulmi suka yi, lamari ne da ke kara irin fatan da ake da shi na farkawar dukkanin al'ummar musulmi na duniya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa a halin yanzu tarihin bil'adama yana fuskantar wani gagarumin sauyi mai girma ne, daga nan sai ya ce: Bil'adama dai sun gwada dukkanin akidu na abin duniya da suka hada da gurguzu, jari hujja, ‘yan kasanci da rashin yarda da Ubangiji, to amma a halin yanzu suna a wani sabon yanayi ne wanda babbar alamar hakan ita ce irin yadda al'ummomi suka koma ga Allah Madaukakin Sarki da kuma neman taimako daga wajen karfi maras karewa na Ubangiji da kuma dogaro da koyarwar Ubangiji.
1089450




















captcha