Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, yan nakalto daga shafin sadarwa na yanar giz o na tashar talabijin din Alkausar cewa, daya daga cikin manyan jami;an gwamnatin Iran ya bayyana cewa gidan talabijin din Alkausar ya taka gagarumar rawa wajen daukar taron kasashen yan ba ruwanmu da aka gudanar a nan brnin Tehran tare da halartar wakilan kasashe 120 mambobi a kungiyar da kuma wakilan kasashe sama da ashirin da suka zo a matsayin yan kallo.
Kasashen Latin Amurka da suka halarci zaman taron kasashen kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM karo na 16 a birnin Tehran sun bayyana cewar zaman taron ya yi armashin gaske. Ministan harkokin wajen kasar Venezuala Niclolas Maduro ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka gudanar da zaman taron kungiyar 'yan ba ruywanmu ta NAM karo na 16 a birnin Tehran, tare da bayyana cewar bayanin bayan taron kungiyar ya samu cikekken amincewar mambobin kungiyar 120 tare da jaddada goyon baya ga shirin makamashin nukiliyar kasar Iran da kafa 'yantacciyar kasar Palasdinu.
Maduro ya kara da cewar zaman taron kungiyar ta NAM karo na 17 za a gudanar da shi ne a kasar Venezuala a shekara ta 2015, sannan kungiyar ta NAM tana kokarin ganin an samar da wata sabuwar duniya da zata gudana ba tare da tasirin kasashe 'yan mulkin mallaka ba. A nashi bangaren mataimakin ministan harkokin wajen kasar Chile Fernando Schmidt ya bayyana cewar zaman taron kungiyar ta NAM karo na 16 ya jaddada bukatar aiwatar da gagarumar gyara a Majalisar Dinkin Duniya, tare da bayyana fatan ganin al'amura sun kyautata a nan gaba.
Haka zalika Jakadan kasar Boliviya a kasar Iran Jorge Miranda ya bayyana gamsuwarsa kan yadda aka gudanar da zaman taron kungiyar ta NAM karo na 16, tare da hadin kan da mambobin kungiyar suka bayar na halartan zaman taron, gami da daidaiton baki da aka samu a tsakaninsu kan dukkanin batutuwan da aka gabatar a bayanin bayan taron kungiyar ta 'yan ba ruwanmu.
1089554