Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo, cewa gwamnatin kasar Algeria za ta dauki nauyin shirya wata gasar karatun kur’ani mai tsarki wanda hakan zai samu halatar makaranta da masana daga sassa na kasashen msuulmi da kuma kasashen larabawa wanda a cewarsa zai bayar da damar bunkasa wannan bangare kamar dai yadda aka fada.
An gudanar da wata zanga-zanga a cikin birnin Alkahira na kasar Masar domin nuna rashin amincewa da salon mulkin Muhammad Morsi tare da kasa aiwatar da abubuwan da yay i wa mutane alkawali a lokacin da yake neman kuri’arsu.
Rahotanni daga birnin Alkahira sun tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun yi ta rera taken nuna rashin amincewa da mulkin Morsi, tare da daga hotunan tsohon shugaban kasar Jama Abdulnasir a matsain wata alama ta kishin larabci da kuma kiyayya da kasashen yamma da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Mohammad Morsi wanda ya lashe zaben shugaban kasar Masar karkashin inuwar kungiyar Ikhwanul Muslim, ya fara shan kakkausar suka daga wani bangare na al’ummar kasar Masar, musamman dangane da yadda kasar Masar ta ci gaba da gudanar da alakarta da haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da wani canji ba, duk kuwa da irin alkawalin da ya dauka na yin nazari kan dangantakar Masar da Isra’ila da kuma batun taimaka ma palastinawa, wanda a halin bayan darewa kan kujerar shugabanci, duk wadannan abubuwa ba su cikin abin da ya sanya a gaba, maimakon haka ma a makon da ya gabata ne ya aike da jakadansa zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila.
1095590