Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar, cewa kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon tana taimaka ma mutanen kasar Syria da suke gudun hijira a kudancin Lebanon bayan da yakin kasar ya sanya suka kauracewa gidajensu domin tsira da rayukansu kamar dai yadda bayanin ya tabbatar a jiya.
A bangare guda kuma an sake bude ofishin tashar talabijin din Al-alam da ke birnin Alkahira na kasar Masar bayan rufe shi na tsawon kimanin mako guda sakamakon matakan da mahukuntan kasar suke dauka na hana kafofin yada labarai masu zaman kansu bayyana hakikanin abin da ke faruwa a kasar musamman a wannan lokaci da zaben shugaban kasa ke kara karatowa.
A lokacin da yake bayyana abubuwan da suka faru, shugaban ofishin na tashar talabijin din Al-alam a birnin Alkahira ya bayyana cewa, babu zato babu tsamani sun ga jami’an tsaro a cikin kayan sarki sun shigo cikin ofishin,inda suka kwashe kayan da ke cikinsa tare da yamutsa su, kuma suka kulle wurin ba tare da yi wa ma’aikatan wurin wani karin bayani ba.
an sake bude ofishin tashar talabijin din Al-alam da ke birnin Alkahira na kasar Masar bayan rufe shi na tsawon kimanin mako guda sakamakon matakan da mahukuntan kasar suke dauka na hana kafofin yada labarai masu zaman kansu bayyana hakikanin abin da ke faruwa a kasar musamman a wannan lokaci da zaben shugaban kasa ke kara karatowa a kasar, wanda bai wuce mako guda ba.
1096161