Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa al'ummar kasar masar na ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewa da batunci ga addinin muslunci da kuma manzon rahma da Amurkawa suka yi ta hanayr nuna wani fim na cin zarafi da izgili ga addinin muslunci a cikin wannan mako kamar dai yadda kowa ya sani.
A yau ma an ci gaba da zanga zangar nuna fushi da majigin nan wanda aka shirya a kasar Amurka mai nuna batanci ga addinin Musulunci a kasashen musulmi da dama.
An gudanar da irin wadannan zanga zanga a kasashen Lebanon Masar Yemen Sudan Tunisa da kuma Syria.
Gidan television na Press Tv mai watsa shirye shiryensa da harshen turanci a nan Tehran ya bayyana cewa an gudanar da zanga zanga a birnin Londan inda dubban musulmi suka nuna fushinsu da wannan majigin na matanci ga addinin mulunci wanda wasu yahuadawa suka shirya a kasar Amurka.
Masu zanga zanga a mafi yawan kasashen musulmi sukan kona tutucin Amurka da kuma
A kasar Pakistan da kuma yankin Kashmir na kasar India ma an gudanar da irin wannan zanga zangar wanda ta yi Allah wadai da gwamnatin kasar Amurka da kuma wadanda suka tsara wannan majaigin.
Har’ila yau Dr Isma’il Salami wani masanin harkokin gabas ta tsakiya fadawa gidan television na Presstv cewa “yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma suke reyawa ba gaskiya bane, don yin wani abu wanda zai cutar da musulmi fiye da biliyon guda da raba a duniya ba yenci ba ne.
1097963