IQNA

Mutanen Lebanon Cikin Fushi Sun Afka Kan Wani dakin Cin Abinci Na Amurkawa

17:49 - September 16, 2012
Lambar Labari: 2412774
Bangaren kasa da kasa, mutanen kasar Lebanon cikin fushi sun gudanar da wata zanga-zanga ta yin Allawadai da fitar da fim din cin zarafin manzon Allah da addinin muslunci da Amurkawa suka yi inda suka afka kan wani dakin cin abinci mallakin Amurkawa da ke arewacin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shfin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar, cewa mutanen kasar Lebanon cikin fushi sun gudanar da wata zanga-zanga ta yin Allawadai da fitar da fim din cin zarafin manzon Allah da addinin muslunci da Amurkawa suka yi inda suka afka kan wani dakin cin abinci mallakin Amurkawa da ke arewacin kasar kamar dai yadda rahoton ya tabbatar.

Majalisar dokokin kasar Yemen ta bukaci sojojin Amurka su fice daga babban birnin kasar Sanaa, majalisar ta bukaci ficewar sojojin ne bayan sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayar na cewa ta aike da sojojinta zuwa birnin Sanaa din bada kariya ga ofishin jakadancinta a can bayan zanga zangar da mutanen birnin suka yi a harabar ofishin a jiya jumma’a. inda suke nuna fushinsu kan majigin nan na batanci ga manzon Musulunci.

Yansanda a kasar ta yemen dai sun kama mutane da dama sun tsare kan zanga zangar nuna fushin da suka yi kan batanci ga Musulunci, har’ila yau an gudanar da zanga zangar nuna fushi ga majigi mai batanci ga Musulunci a birnin Sudney na kasar Australia a gaban ofishin jakadanci na kasar Amurca da ke can. Yan sanda sun kama mutane da dama wasu kuma sun ji rauni a lokacinda yansanda suka yi kokarin tarwatsa taron.

Hakama majalisar dokokin kasar Afganistan ta yi Allah wadai da majigin wanda yake muzanta manzon Allah (s), kuma ta bukaci kasar Amurka ta haramta majaigin ta kuma gurfanar da wadanda suke da hannun wajen yin sa.

1098048









captcha