IQNA

Hankoron Kona Wani Masallaci A Faransa Wasu Masu Kiyayya Da Muslunci Na

17:49 - September 16, 2012
Lambar Labari: 2412780
Bangaren kasa da kasa, wasu masu tsananin kiyayya da addinin muslunci a kasar suna ta hankoron banka wuta a kan wani masallaci mallakin muslumi a kasar musamman ma bayan da musulmi suka fara mikewa domin kare mutuncin addinin daga masu hankoron muzguna masa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alalam, cewa wasu masu tsananin kiyayya da addinin muslunci a kasar suna ta hankoron banka wuta a kan wani masallaci mallakin muslumi a kasar musamman ma bayan da musulmi suka fara mikewa domin kare mutuncin addinin daga masu hankoron muzguna masa ta hanyar abubuwa na batunci.

Masu fafutukar kare hakkin bil adama a kasar Bahrain sun fitar da wani bayani da ke yin Allawadai da irin matakan da masarautar kasar take dauka na yin amfani da karfi wajen murkushe fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana.

Bayanin ya ce akwai mutane sun kusa kai dubu biyu da yanzu haka mahukuntan Bahrain suke tsare da su babu gaira ba sabar, saboda kawai dalilai na siyasa, daga cikin wadanda mahukuntan Bahrain suka kame akwai kanan yara kimanin 240, wasu daga cikinsu shekarunsu ba su wuce11 zuwa 12 ba, kamar yadda suka kashe sama da mutane 60 ta hanyar azabtarwa a gidajen kaso.

Baynin ya kirayi sauran kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa das u dauki kwararn matakai daidai da kaidoji da dokoki nakasa da kasa domin ladabtar da mahukuntan kasar Bahrain kan cin zarafin da suke yi kan fararen hula marassa kariya, tare da cikakken goyon bayan Amurka da sauran kasashen yammacin turai.

1098401










captcha