IQNA

Dubban Masallata A Kasar Iraki Sun Yi Allawadai Da Fim Din Batunci Ga Musulunci

17:48 - September 16, 2012
Lambar Labari: 2412781
Bangaren kasa da kasa, dubban musulmi a kasar Iraki da suka gudanar da Sallar Juma'a sun yi Allawadai dad a kakkausar murya kan fitar da fim din batunci da Amurkawa suka yi a cikin wannan mako wanda ya jawo zanga-zanaga adukaknin kasashen musulmi na duniya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na swissinfo, cewa dubban musulmi a kasar Iraki da suka gudanar da Sallar Juma'a sun yi Allawadai dad a kakkausar murya kan fitar da fim din batunci da Amurkawa suka yi a cikin wannan mako wanda ya jawo zanga-zanaga adukaknin kasashen musulmi na duniya kuma hakan na ci gaba da bazuwa.

Dubun-dubatar al'ummar Iran sun fito kan tittuna domin yin Allah wadai da fim din cin zarafin addnin musulunci, zangz-zangar da aka yi a cikin brining Tehran da kuma dukkanin biranen Iran ta maida hankali ne akan yin tir da wadanda su ka shirya fim din na cin zarafin musulunci tare da yin kira ga kasar Amerika da ta nemi gafarar musulmi.

A jawabin da aka karanta bayan kare-zangar, an dora alhakin abinda ya faru ga Amarika da Birtaniya da kuma 'yan sahayoniya na duniya.
Bugu da kari bayanin ya ce;a binda ya faru wata makarkashiya ce wacce ta ke nuni da kiyayya ga addinin musulunci da musulmi.

Har ila yau, jawabin ya yi kira da a hukunta wadanda su ked a hannu wajen shirya fim din na cin zarafi.

1097906






captcha