IQNA

Mutanen Birnin Birnin Istanbul Sun Yi Allawadai Da Fitar Fim Din Batunci Ga Muslunci

17:48 - September 16, 2012
Lambar Labari: 2412783
Bangaren kasa da kasa, dubban musulmi sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Istanbul na kasar Turkiya domin la'antar kasar Amurka dangane da fim din batuncin da aka shirya a kasar domin cin zarafin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa dubban musulmi sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Istanbul na kasar Turkiya domin la'antar kasar Amurka dangane da fim din batuncin da aka shirya a kasar domin cin zarafin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da kuma tozarta addini.

A kalla mutane shida ne su ka rasa rayukansu a kasashen Sudan da Tunisya a yayin zanga-zangar nuna kin jinin fim din Amerika na cin zarafin musulunci.

Masu zanga-zanga a birnin Khartum sun haura katangun ofisoshin jakadancin Jamus da Birtaniya tare da cinna wuta a wasu sassa nasu kamar yadda rahotanni su ka ambata.

Har ilayau masu zanga-zangar sun tasamma ofishin jakadancin Amerikan da ke birnin Khartum domin kona shi, sai dai jami'an tsaro sun shiga tsakaninsu.

Rahotanni sun ambaci cewa a kalla mutane uku su ka rasa rayukansu saboda bude musu wata da jami'an tsaro su ka yi.

A birnin Tunis wanda har yanzu a ke ci gaba da bata kasha tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro, mutane uku ne su ka kwanta dama.

Masu zanga-zangar dai sun haura katangar ofishin jakadancin Amerikan tare da sauke tutarsa da kuma daga wata bakar tuta mai dauke Kalmar shahada.

A kasar Masar kuwa kungiyar 'yan'uwa musulmi ta janye kiran da ta yi wa mutane su fito zanga-zanga saboda kaucewa rikici.

Tun a shekaran jiya ne dai masu zanga-zangar ke kokarin kutsawa cikin ofishin jakadancin Amerikan, sai dai jami'an tsaro sun hana su.
Daga daren jiya zuwa safiyar yau, an gina katangar da ta killace ofishin jakadancin Amerika a birnin alahira.

1098346






















captcha