Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lexpress, cewa masu tsanannin adawa da addinin muslunci a kasar Jamus sun kudiri aniyar watsa fim din batunci ga manzon Allah wanda Amurkawa suka shirya da nufin muzunta addinin muslunci da manzon rahma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalan gidansa tsarkaka kamar dai yadda duniya ta sheda.
Gungun lauyoyi musulmi sun gudanar da wani zama na musamma a birnin maskat fadar mulkin kasar Oman domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa domin kare hakkokin fararen hula.
Daga cikin wadanda suka halarci taron har da wakilai daga kasashen Iran, Yeman, Saudiyya, Lebanon, Morocco, Tunisia, Turkiya, Aljeria, Libya, Oman da kuma Qatar, wadanda dukakninsu mambobi ne akungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, wadda ta take wakiltar musulmi a taruka na kasa da kasa.
Kungiyar lauyoyi musulmi sun gudanar da wani zama na musamma a birnin maskat fadar mulkin kasar Oman domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa domin kare hakkokin mutane, duk kuwa d cewa ra’ayoyi kan boren larabawa sun sha banban.
1099147