IQNA

Kasar Jamus Ta Hana Tsinan Mutumin Nan Na Amurka Mai Cin Zarafin Addini Shiga Kasarta

17:39 - September 18, 2012
Lambar Labari: 2414560
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Jamus a hukumance ta hana mutumin nan na kasar Amurka da ke cin zarafin addini shiga cikin kasarta sakamakon bakin jinin day a jawo ma kasar bayan day a kona kur'ani a sheakarar da ta gabata a wannan karon kuma ya fitar da wani fim domin wulakanta manzon Allah.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tf1 cewa gwamnatin kasar Jamus a hukumance ta hana mutumin nan na kasar Amurka da ke cin zarafin addini shiga cikin kasarta sakamakon bakin jinin day a jawo ma kasar bayan day a kona kur'ani a sheakarar da ta gabata a wannan karon kuma ya fitar da wani fim domin wulakanta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Sojojin Siriya suna ci gaba da tsarkake yankunan kasar daga 'yan ta'adda tare da halaka da dama daga cikin 'yan ta'addan a yau litinin kafar watsa labaran gwamnatin Siriya "Sana" ta bayyana cewar a yau litinin sojojin kasar sun kai farmaki kan yankin Saifud Daula da ke garin Halab da yankin da ke kusa da kan iyaka da kasar Turkiyya, inda suka yi nasarar halaka 'yan ta'adda da dama, tare da kwasan ganimar makamai manya da kanana da aka shigo da su cikin kasar daga kasashen ketare domin karfafa ayyukan ta'addanci a kasar.

Har ila yau sojojin kasar ta Siriya sun kaddamar da hare hare kan tawagar 'yan ta'adda a yankin Babul da ke garin Halab inda suka kashe 'yan ta'adda 34. Haka nan sojojin gwamnatin Siriya sun tarwatsa wata wasu motoci da suke dauke da 'yan ta'addan a yankin Kufru Humur. Kamar yadda sojojin suka kai farmaki wata maboyar 'yan ta'addan a yankin Al-Fara'yah da ke garin Hama, inda suka halaka 'yan ta'adda akalla 8 tare da jikkata wasu da dama, kuma wasu daga cikin 'yan ta'addan sun mika kansu ga sojojin.

1100084

captcha