Bnagaren kasa da kasa, an fara gudanar da zaman taro na gidajen talabijin da radio na kasashen musulmi a birnin Tehran wanda yake samun halartar wakilai daga kasashen ketare da suka zo domin bayyana irin ayyuakna da suke gudanarwa abnagarori na yada ilmi da al'adun muslunci da kuma wayar da kan musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa tun jiya an fara gudanar da zaman taro na gidajen talabijin da radio na kasashen musulmi a birnin Tehran wanda yake samun halartar wakilai daga kasashen ketare da suka zo domin bayyana irin ayyuakna da suke gudanarwa abnagarori na yada ilmi da al'adun muslunci da kuma wayar da kan musulmi kan lamurra da suke da dangantaka da musulmi baki daya.
Ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da karfin kalubalantar duk wata barazana da take fuskanta daga makiya.
A zantawar da ya yi da manema labarai a birnin Isfahan na kasar Iran a yau litinin; Ministan tsaron kasar Iran Brigadier Janar Ahmad Wahidi ya bayyana cewar gudanar da zaman babban taron kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM karo na 16 a Iran lamari da ke fayyace cewa kasar ta Iran ba ta girgiza ba a fuskar tsaro, karfi da siyasa saboda barazanar harin wuce gona da iri da take fuskanta ko matsin lambar da makiya ke mata a fuskar tattalin arzki da siyasa.
Janar Wahidi ya kara da cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta karbi ragamar jagorancin kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM na tsawon shekaru uku, kuma tana da karfin gudanar da kungiyar ta NAM tare da haifar da gagarumin canji a cikinta.
1100110