IQNA

Dubban Musulmi A kasar Girka Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kare Martabar Manzo

23:31 - September 25, 2012
Lambar Labari: 2419841
Bangaren kasa da kasa, dubban musulmin kasar Girka sun gudanar da wani gagarumin jerin gwano a birnin Athen na kasar wanda ya samu halartar dubban musulmi domin nuna fushinsu kan cin zarafin da ake yi wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare da iyalan gidansa tsarkaka a kasashen turai.
Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, a jiya dubban musulmin kasar Girka sun gudanar da wani gagarumin jerin gwano a birnin Athen na kasar wanda ya samu halartar dubban musulmi domin nuna fushinsu kan cin zarafin da ake yi wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare da iyalan gidansa tsarkaka a kasashen turai musamman fin din batuncin da aka fitar cikin kwanakin nan.
A can kasar Masar kuwa wahabiyawan kasar sun kawafa wani kwamiti na umurni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna wanda da dama daga cikin al’ummar kasar suka yi Allawadai da shi kamar yadda ita ma jami’ar Azhar kan kafa wannan kwamiti domin aiwatar da manufar wata kasa da ke bin akidar wahabiyanci da ke yankin.
Al’ummar kasar Masar dai suna zargin gwamnatin kasar saudiyya da hannu kai tsaye wajen taimaka wa ‘yan salafiyya da ke bin akidar wahabiyanci, kuma abin da yake faruwa yanzu haka a kasar ya tabbatar da wannan aniya ta wahabiyawan.
Jama’ar wahabiyawan kasar Masar sun kawafa wani kwamiti na umurni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna wanda da dama daga cikin al’ummar kasar suka yi Allawadai da shi kamar yadda ita ma jami’ar Azhar kan wannan batu.

1105746





















captcha