Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-kut, cewa da dama daga cikin masana suna ganin cewa hanyoyin yada labarai na kasashen musulmi za su iya taka gagarumar rawa wajen wayar da kan musulmi kan muhimamna bubuwa da suke faruwa a duniyar musulmi musamman ma kan batun p[alastinu da kuma halin da al’ummar wannan yanki suke ciki a wannan lokaci da Amurka take shimfida ikonta.
Dan majlaisar dokokin kasar Lebanon daga gugun ‘yan majalisa na kungiyar hizbullah Nawwaf Musavi ya yi kira da a warware matsalar kasar Syria ta hanyar lumana maimakon kara zuzuta wutar rikicin da ake gani yanzu haka daga wasu kasashen larabawa.
Babban mai baiwa shugaban kasar Algeria shawarwari kan harkokin siyasa ya yi kakkausar suka kan kungiyar hadin kan kasashen larabawa dangane da matakin da ta dauka kan rikicin kasar Syria.
Jaridar kasar Syria ta habarta cewa, a zantawar da ta yi da babban mai baiwa shugaban Algeria shawara kan harkokin siyasa Abdulaziz Bilkhaddam ya bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta tafka babban kure dangane da matakin da ta auka kan rikicin kasar, inda take neman agaji daga kasashe makiyan larabawa da su taimaka mata domin kawo karshen gwamnatin Syria, y ace maimakon haka da ya kamata kungiyar kasashen larabawa ta taimaka wajen warware rikin ne ta hanyar dukkanin bangarori zuwa tattaunawa, ba goyon bayan 'yan adawar Syria da suke dauke da makamai ba.
1105962