Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Sayyid Sadruddin Kubanchi babban limamain masallacin Najaf mai alfarma ya yi kakusar suka danganre da yadda majalisar dinkin duniya take nuna halin ko in kula kan keta alfarmar addinai da wasu ke yi duk kuwa da cewa hakan ya sabawa dukaknin dokoki na duniya baki daya.
A wani baynin kuma an gudanar da taron baje klin kur’ani a India, a wajen taron na bajen kolin an nuna kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki wadanda aka rubuta da hannu a kasashen musulmi daban-daban, haka nan kuma wadanda aka buga su a kasashen musulmi, da nufin kara fito da matsayin wannan littafi mai tsarki, tare da bayyanawa duniya cewa matsayinsa yana damfare ne da rayuwar mabiya addinin muslunci, domin ya zama hannunka mai sanda ga masu keta alfarmarsa.
Gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar Pakistan inda ake nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibiyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor na kasar, na dag acikin muhimamn ayyuka da gwamnatin kasar pakistan ke aiwatarwa akowace shekara. Amma a wannan shekara lamarin ya dauki sabon salo na kara kawata taron, da kuma yawan kur’anan da ake nunawa.
1109494