Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV, cewa ministocin harkokin wajen kasashen musulmi sun gudanar da zama domin tattauna muhimamn batutuwa da suka danganci cin zarafin da ake yi wamusulmi tare da bata sunan addinin muslunci ta hanyar tozarta manyan abubuwa da yake tsarkakewa musamman manzo da kur’ani.
Sabuwar dokar da aka kafa a kasar Saudiyya dangane da wajabta ma mutane dakatar dukkanin ayyukansu a lokacin salla a kasar Saudiyya hakan ya jawo rikici a tsakanin mutanen kasar da kuma mahukunta, sakamakon matakan da gungun mutanen da ake kira masu hani daga mummna da umurni da kyakkayawa suke aikatawa da sunan suka kare addini tare da izini daga masarautar wahbaiyawan kasar.
A lokacin da malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mabiya addinai kamar majamioin mabiya addinin kirista.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
Masana da dama suka ganin a lokacin malaman addinin muslunci na hakika suke ci gaba da hankoron ganin an samu fahimtar juna tsakanin dukaknin al’ummomin duniya tare da zaman lafiya wasu daga cikin masu kiran kansu malaman addini a kasar Sudiyya suna fitar da fatawoyin halascin kai hari kan saura mutane da ba musulmi ba.
1109273