IQNA

Wajibi ne Kan Kafofiin yada Labarai Su Taka Rawa A Bangaren Kare Addinai

17:02 - October 01, 2012
Lambar Labari: 2423853
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya bayyana cewa ya zama wajibi kafofin yada labarai na kasashen musulmi su taka gagarumar rawa wajen yaki da munan akidu na yaki da sauran addinai da wulakanta su musamman amsu cin zarafin addinin muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC, Ikmaluddin Auglo babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya bayyana cewa ya zama wajibi kafofin yada labarai na kasashen musulmi su taka gagarumar rawa wajen yaki da munan akidu na yaki da sauran addinai da wulakanta su musamman amsu cin zarafin addinin muslunci a kasar Amurka da turai.
Ofishin shugaban kasar Tunisia ya fitar da wani bayani da acikinsa yake bayyana cewa yin wasu kalamai na keta alfarmar addinin muslunci ba shi ne ma’anar fadin albarkacin baki ba kamar yadda wasu suka dauka kuma suke amfani da wannan damar domin cin zarafin musulmi a cikin kasar da ma wajenta.
Baynain ya ce dole kowa ya girmama addinin kowane bangare a cikin dokokin kasar Tunisia, musulmi ba shi da hakkin ya ci zarafin wani saboda shi ba musulmi ba ne, kamar yadda wani wanda ba musulmi ba ba shi da ahhaki ko hurumin cin zarafin muslmi, haka nan kuma ko da musulmin ne ba shi da hakkin ya yi kalaman batunci kan akidar musulmci saboda wasu ra’yoyi nasa, yin hakan ya saba ma kundin tsarin mulki.
A cikin wannan makon ne ofishin shugaban kasar Tunisia ya fitar da wani bayani da acikinsa yake bayyana cewa yin wasu kalamai na keta alfarmar addinin muslunci ba shi ne ma’anar fadin albarkacin baki ba kamar yadda wasu suka dauka, domin kuwa fadin albarkacin baki baya nufin tozarta wani ko mahanagarsa.
1109433



















captcha