Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa jamia’n tsaron kasar Bahrain sun afka kan fararen hula masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi ta hanyar lumana wanda kuma dama hakan na daya daga cikin hanyoyin da gwamnatin kasar ta fara amfani da su domin murkushe duk wani yunkurin da ke neman sauyi na siyasa.
An shirya kara da za agabatar a gaban shari’a kan wasu yahudawan sahyuniya masu wulakanta kur’ani mai tsarki a cikin yankunan palastinawa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye domin tabbatar musu da cewa musulmi ba za su amince da abin da uke yi ba na keta alfarma kur’ani da sauran ababe masu alfarma a cikin addinin muslunci.
A bangare guda kuma a ci gaba da mayar da martanin da malaman addinin muslunci gami da masana suke yi kan malamin gwamnatin Qatar Yusuf Kardawi, ministan mai kula da harkokin addinin muslunci a palastinu Muhmud Habbash ya bayyana cewa fatawar da Yusuf Kardawi ya bayar da ke hana sauran musulmi ziyartar masallacin Qods mai alfarma ta sabawa koyarwar alkur’ani mai tsarki da kuma sunanr manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
A kwanakin baya ne Yusuf Kardawi da ake kallonsa amtsayin daya daga cikin mamalan duniyar sunna, kuma daya daga cikin malaman da suka taka rawa a baya domin ganin sun wayar da kan muslulmi kan babbar barazanar da ke tattare da kulla alaka da musulmi suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, amma a halin yanzu ya zama malamin fadar sarkin Qatar, inda yake bayar da fatawowyi da suka yi daidai da abin da sarkin kasar ke bukatar ji, kasantuwarsa daya daga cikin karnukan farautar yahudawan sahyuniya.
1109095