IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Masallacin Qods

17:00 - October 06, 2012
Lambar Labari: 2426770
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar hizbullaha a kasar Lebanon ta yi Allawadai da ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila kan masallacin Qods mai alfarma wanda hakan ya yi sanadiyyar jikkatar daruruwan palastinawa massalata da suka halarci masallacin domin yin sallar juma’a.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kungiyar gwagwarmayar hizbullaha a kasar Lebanon ta yi Allawadai da ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila kan masallacin Qods mai alfarma wanda hakan ya yi sanadiyyar jikkatar daruruwan palastinawa massalata da suka halarci masallacin domin yin sallar juma’a a jiya.
Wani rahoton na daban kuma ya ce ma'aiakatar harkokin wajen kasar Rasha ta gargadi gwamnatin kasar Turkiyya da ta guji kara kunna wutar rikici a yankin gabas ta tsakiya. Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha a yau asabar ta fitar da bayani da a ciki ta bukaci gwamnatin Turkiyya da ta dauki matakin juriya da hakuri kan matsalar harba makaman roka-roka da aka yi cikin kasarta daga kasar Siriya, musamman kasancewar akwai rudani dangane da wadanda suke da hannu wajen harba rokokin.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta kara da cewar matakan da gwamnatin Turkiyya take dauka kan kasar Siriya lamari ne da zai kara janyo tabarbarewan al'amura a dukkanin yankin. Har ila yau bayanin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ya yaba kan matakin da gwamnatin Turkiyya ta dauka na gabatar da kokenta ga kungiyar kasa da kasa, tare da jaddada muhimmancin warware matsalar ta hanyar lumana.
1113575




captcha