IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Kakkausar Suka Dangane Da Cin Keta Alfarmar Masallacin Qods

16:36 - October 08, 2012
Lambar Labari: 2428095
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen msuulmi ta yi kakakusar suka da yin Allawdai da cin zarafin zarafin da yahudawan sahyuniya suke yi kan al’ummar palastinu a cikin kwanakin nan musamman ama birnin Qods da kewaye inda suke cin Karensu babu bababka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa kungiyar kasashen msuulmi ta yi kakakusar suka da yin Allawdai da cin zarafin zarafin da yahudawan sahyuniya suke yi kan al’ummar palastinu a cikin kwanakin nan musamman ama birnin Qods da kewaye inda suke cin Karensu babu bababka tare da goyon bayan siyasa da suke samu daga manyan kasashen turai.
A bangare guda kuma wasu tsagerun yahudawan sahayoniya 'yan kaka gida suna ci gaba da kai hare hare kan Palasdinawa tare da musguna musu a yankunan da suke gabar yammacin kogin Jordan. Kafar watsa labaran Palasdinawa ta Wafa ta bayyana cewar a yau asabar tsagerun yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida sun kai farmaki kan Palasdinawa tare da lalata musu gonaki ta hanyar sare bishiyoyin 'ya'yan marmari da yawansu ya kai 120 a yankin Alkhadar da ke kudancin garin Baitu- Laham a gabar yammacin kogin Jordan.
Har ila yau tsagerun yahudawan sahayoniyyan 'yan kaka gida sun kai farmaki kan kauyen Kufru-Kadoum da ke gabar yammacin kogin na Jordan da nufin barnata gonakin Palasdinawa, amma al'ummar kauyen sun kalubalance su lamarin da ya janyo dauki ba dadi a tsakanin bangarorin biyu. A mafi yawan lokuta sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna yin rakiya ga tsagerun yahudawan tare da katangen Palasdinawa da suke kokarin hana yahudawan barnata musu gonaki.
1114720






captcha