Bnagaren kasa da kasa, baban limamin yankin Katitf na gabacin kasar Saudiyya ya yi kakkausar suka dangane da yadda azzaluman mahukuntan kasar suke daukar wasu matakai na rashin imani da takurawa kan masu nema sauyi ta hnayr lumana a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, baban limamin yankin Katitf na gabacin kasar Saudiyya ya yi kakkausar suka dangane da yadda azzaluman mahukuntan kasar suke daukar wasu matakai na rashin imani da takurawa kan masu nema sauyi ta hnayr lumana a kasar da ke tinkaho da goyon bayan Amurka.
Tuni dai jami’an tsaro na Iran din suka gano irin wadannan mutanen da saboda wata manufa da suke da ita suka yi kokarin dagula lamurra a cikin gidan da nufin biyan bukatar makiyan sannan kuma aka sami nasarar kama wasu daga cikinsu lamarin da ya zuwa yanzu ana iya cewa ya fara haifar da da mai ido don kuwa tuni darajar kudin kasar ta fara dawowa yadda take sannan kuma jama’a suka fara fahimtar inda matsalar take. Irin wannan yanayin ne ma ya sanya wasu masanan kasashen yammaci suka fara ba wa ‘yan siyasar nasu shawarwarin cewa kara matsin lamba da sanya takunkumi a kan Iran ba abin da zai haifar in ba kara hadin kan al’ummar kasar wanda hakan lamari ne mai karfafa jami’ai da kuma gwamnatin kasar.
Ko shakka babu dubi cikin tarihin shekaru 33 da suka gabata na Iran wato tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar lamari ne da ke tabbatar da cewa matsin lamba irin wannan da kuma farfaganda sun gaza wajen sanya al’ummar Iran da jami’an kasar mika wuya kuma a wannan karon ma ba za su cimma wannan manufa da suke son cimmawa ba. Na’am babu shakka kasashen yammacin za su ci gaba da kokarin da suke yi sannan kuma kafafen watsa labaransu za su ci gaba da yada kararraki da kuma kanbama abin da ke faruwan, amma ko shakka babu al’ummar Iran din sun san abin da makiyan na su suke son cimmawa don haka ba za su taba barin makiyan su cimma wadannan manufofi ba kamar yadda ba su bar su sun cimma manufofin da suke da su a baya ba.
1114315