IQNA

Fiye da maniyyata miliyan biyu ne su ka isa birnin makka mai alfarma domin fara gudanar da ayyukan haji.

15:37 - October 24, 2012
Lambar Labari: 2437513
Fiye da maniyyata miliyan biyu ne su ka isa birnin makka mai alfarma domin fara gudanar da ayyukan haji.
MKamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa;aniyyatan suna taruwa ne gungu-gungu a karkashin tutocin kasashensu suna masu sanye da harami domin isa saharar mina a matsayin ranar tarwiyya.
A gobe ne kuma maniyyatan za su yi tsayuwar arfa wanda shi ne rukuni mai tushe na aikin haji. Daga nan kuma maniyyatan za su nufi Muzdalifa da marecen gobe alhamis inda za su tsinci duwatsun jifar shadan. Daga nan ne kuma za su koma zuwa mina a ranar salla domin yin jifar shaidan na "jamratul-Kubrah" da yin hadaya da aski ko saisaye da dawafi a ka'aba da kuma safa da marwa."
Ranakun asabar da lahadi da litinin ne za su zama "Ayyaut-tashriq" da ake yin jifar shaidan sau uku a cikinsu sannan kuma a karkare aikin hajin da dawafin ban kwana.


1125055
captcha