IQNA

15:26 - October 27, 2012
Lambar Labari: 2438571
Kamar sauran kasashen duniya da kungiyoyi na kasa da kasa kasar faransa ma ta yi Allah wadai da hari ta'addancin da ta kai wa fararen hula palasdinawa.
A ci gaba da yin Allah wadai da harin da jiragen yakin HKI suka kai wani kamfanin kera makamai na kasar Sudan, kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kakkausar suka ga wannan danyen aiki na HKI wanda tace keta hurumin kasar Sudan din ne.

Shugabar hukumar Tarayyar Afirkan Madam Nkosazana Dlamini-Zuma a yayin wata ganawa da ta yi da wakilin kasar Sudan a kungiyar Tarayyar Afirkan ta ce wannan harin yin karen tsaye ne wa dokokin kasa da kasa tana mai jaddada wajibcin girmama hurumin kasar ta Sudan.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Sudan din Umar Hasan al-Bashir ya bayyana cewar wannan harin yana nuni da irin damuwar da HKI take ciki ne sakamakon irin ci gaban da kasar Sudan din take samu, yana mai cewa ko da wasa hakan ba zai kawar da gwamnatinsa da al’ummar kasar daga tafarkin da suka rika na tabbatar da ‘yanci da kuma aiwatar da koyarwar addinin Musulunci ba.

A ranar larabar da ta gabata ce ministan yada labaran kasar Sudan din ya sanar da cewa jiragen yakin HKI guda hudu ne suka kai wa wannan kamfanin hari da ya yi sanadiyar ruguza shi.

1126709
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: